Tattaunawar kungiyar PSG dangane da batun tsawaita wa’adin Messi

0
55

Kungiyar Paris SG ta shiga tattaunawa” kan tsawaita kwantiragin fitaccen dan wasanta Lionel Messi na Argentina, wanda yarjejeniyarsa ke karewa a watan Yuni 2023, labarin da  Luis Campos mai ba da shawara kan harakokin kwallon kafa na PSG ya tabbatar a yau lahadi.

Shugabanin kungiyar ta PSG sun bayyana fatan Messi zai  ya ci gaba da PSG,duk da cewa suna cikin tattaunawa, dan wasan mai shekara 35, da kuma ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai dole ne ya yanke shawarar abin da makomarsa za ta kasance, ‘yan makonni bayan ya kai ga lashe gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.

Messi ya koma PSG ne a shekara ta 2021, na tsawon shekaru biyu, bayan ya shafe tsawon shekaru Barcelona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here