Kotu ta hana CBN tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira

0
212

Wata babbar kotu a babban birnin tarayya, ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN, daga kara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi na naira.

Kotun ta kuma umurci CBN da ya aiwatar da sabon tsarin Naira.

Alkalin kotun Eleojo Enenche, ya bayar da umarnin ne yayin da yake yanke hukunci a cikin wata kara mai lamba FCT/HC/CV/2234/2023, ranar Litinin.

 

“An ba da umarnin wucin gadi na hana duk wani ko wasu ko su kansu, wakilan ma’aikata, jami’an bankuna masu shiga tsakani ko kuma duk wanda zai dakatar ko ya sa a tsawaita, ko ya bambanta ko kuma ya tsoma baki wajen sa a tsawaita ranar da za a daina amfani da tsofaffin kudi na N200, N500, N1000 kamar yadda a ka sa ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023, ana jiran sauraron karar da kuma yanke hukunci kan sanarwa,” in ji kotun.

Babban bankin na CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin canza tsohon kudi na naira da wadanda aka yi wa kwaskwarima.

CBN ya sake fasalin N200, N500, da N1000.

A cikin koke koken da jama’a ke yi na karancin Naira, babban bankin ya kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here