HomeLabaraiShugaban INEC ya gana da mataimakan shugabannin jami’o’i

Shugaban INEC ya gana da mataimakan shugabannin jami’o’i

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gana da mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya gabanin babban zaben 2023.

A halin da ake ciki, shugaban na INEC ya jaddada cewa zaben 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.

Yakubu ya bada wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya a ranar Alhamis.

Ya kuma bukaci mataimakan shugabannin da su yi cikakken bincike domin kaucewa daukar ma’aikatan da ke da alaka da jam’iyyun siyasa da tarihin  bangaranci kafin mika sunayensu ga hukumar.

Shugaban na INEC ya kuma ba da tabbacin cewa za ta fara gudanar da nata binciken sunayen da jami’o’in suka tura domin gudanar da zaben.

Yakubu ya kawar da fargabar da wasu daga cikin VC suke da shi na rashin tsaro, yayin da ya tabbatar da cewa an tsara tsare-tsare masu inganci don kare lafiyar dukkan ma’aikata, kafafen yada labarai, ’yan kungiyar matasa da sauran jami’an zabe.

A cewarsa, adadin masu kada kuri’a (sama da miliyan 93) na zaben 2023 ya fi wadanda suka yi rijista a Afirka.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here