Gwamnatin Lagos ta fara rabon abinci kyauta saboda rashin Naira

0
29

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana samar da rumbunan abinci a sassan jihar, domin rarraba kayayyakin abincin ga iyalai marasa karfi da suka shiga halin kaka-ni-kayi  sakamakon tasirin matsalolin karancin Naira da man fetur.

Yayin sanar da daukar matakin samar wa jama’ar sassauci, gwamna Sanwo-Olu ya sha alwashin daukar matakin ladabtarwa kan dukkanin wadanda suka yi yunkurin amfani da shirin rabon abincin wajen tayar da tarzoma.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin rage kashi  50 cikin 100 na kudin da ake biya akan sufurin ababen hawa mallakin gwamnati, da suka hada da motoci kanana da manya na BRT da kuma jiragen ruwa, umarin da ya ce ya fara ne daga yau  Alhamis.

Sanwo-Olu ya ce hakan zai taimaka matuka wajen sassauta matsin da mazauna Legas suka shiga a sakamakon matsalolin karancin Nairar da aka  sabunta, da kuma rashin wadata da tsadar man fetur.

Daga karshe gwamnan na Legas ya bai wa dukkanin gidajen man fetur da ke fadin jihar, da su  fara aikin sayar da fetur din tsawon sa’o’i 24, domin kawo karshen jerin gwanon da mutane ke shafe awanni ko kwanaki da dama suna yi domin kawai  neman sayen makamashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here