“Jarumi Adam A Zango bai saki matar sa ba”

0
34

Shahararren jarumin nan na fina-finan Hausa na Kannywood, Adam A. Zango bai saki matar sa ba kamar yadda rahotannin da ake yadawa suka bayyana hakan.

A jiya ne dai jarumin ya saki wani faifan bidiyo inda yake bayyana irin sabanin da suka samu da matar tasa.

A cikin bidiyon, jarumin, wanda yake zaune a jihar Kaduna ya bayyana irin matsalar dake tsakanin sa da matarsa, inda ya ce matar tasa ta zabi sana’a a maimakon zaman aure sannan ya yi alkawarin cewa al’umma za su ji labari mara dadi, abin da al’umma suke zargi kamar sakin ta zai yi.

Sai dai bayanan da muka samu daga sahihan majiyoyi sun nunar da cewa sakin bai tabbata ba.

Sannan jarumin ya bayyana cewa abu ne mai wahala ya sake yin aure saboda irin tarin matsalolin da yake fuskanta.

Ana yawan zargin jarumin, Adam A. Zango dai da yawan yin aure-aure da rabuwa da matan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here