Bambancin halin da ‘yan Najeriya suka shiga a canjin kudin Buhari na farko da na biyu

0
47

A daidai lokacin da kotun koli ta bayar da hukunci dakatar da wa’adin daina karbar tsofaffin kudade da Babban Bankin Nijeriya ya bayar a ranar 10 ga watan Fairaru 2023, mutae da ci gaba da kokawa da halin kunci na rashin kudi a sassan Nijeriya, wannan ya tuna mana da ir8in halin da al’umma suka shiga a shekarar 1983 lokacin da Shugaba Buhar ya kaddamar da canjin kudi a lokacin yana Shugaban Nijeriya na mulkin soja.

Wakilinmu Khalid Idris Doya ya yi dubi da kwatanci da irin halin da aka shiga yanzu da kuma yadda mutane suka shiga a da, da farko ya tuntubi Shehin malami kuma masani a bangaren tattalin arziki (Economy), Farfesa Ahmad Sanda, da ke aiki a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato a tsangayar nazarin tattalin arziki kuma tun da ya fara a aiki a jami’ar 1987 har zuwa yanzu yana koyarwa a tsangayar nazarin tattalin arziki, ya shaida cewar canjin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a 1983 ya janyo dogon layi ga jama’a kuma jama’a da dama sun tafka asara sakamakon karancin lokacin lokacin da aka ware wa jama’a. 

Ya misalta banbancin da sauyin kudin mulkin Buhari na farko da na biyu da cewa da can babu ATM ko POS balle mutane su je su nemi kudi a duk lokacin da suke so dole sai sun bi doyon kafin su samu kudade.

Ya ce, “Zan iya tunawa lokacin muna dalibai a Jami’a lokacin da aka yi canjin kudi na 1983, a lokacin dai ka ga babu ATM dole kowa zuwa yake ya bi layi, sannan lokacin da aka bayar bai wadatar ba har zuwa lokacin da aka rufe wasu ba su samu damar shigar da kudadensu ba.

Amma ba zan iya tuna abubuwan da suka faru sosai da sosai ba a wancan lokacin ba.

“Amma ba na da data din yawan asarar da aka yi a wancan lokacin da wannan.”

“A da can baya kamar yadda na fada maka an sha dogayen layi zuwa canjin kudin. A lokacin mu muna da tafiya zuwa Benin, sai da muka tabbatar mun samu sabbin kudade a lokacin kafin muka kama hanya. Tabbas mutane sun yi asara sosai a wancan lokacin saboda ba a bayar da cikakken lokaci don jama’a su je su canza kudinsu ba.”

Kan alfanun canjin kudin ga tattalin arzikin kasa kuwa, ya ce, “Idan na sanya kudina a cikin gida a cikin rami ko karkashin katifa, babu wanda zai yi amfani da kudaden.

Amma idan na kaisu banki, banki na iya ranta ma wasu su fadada sana’o’insu, ka ga su, sun samu dama su bunkasa aikinsu, su dauki mutane aiki tattalin arziki ya samu cigaba. Don haka ta hanyar sauya kudi ana iya kyautata tattaki.”

Ya kuma ce sauyin kudin zai kawo gyara ga matsalar tsaro da na ‘yan bindiga dadi, saukaka harkokin kasuwanci da cinikayya, kana zai rage cin hanci da rashawa, yana mai cewa, “Sannan kowa ya sani ‘yan bindiga dadi masu garkuwa da mutane ba su bada ‘account number’ su ce a yi musu transfer, idan suka ce a musu transfer ka ga sun kai kansu da kansu ke nan.

To, idan mutane ba su da kudade a hannunsu, yanzu misali, a kauyenmu Korama idan aka ce ana son naira miliyan guda (tsabar kudi) ba a samu, saboda babu masu kudi a hannu a halin yanzu, kudi na banki. Da a ce za a iya daurewa kowa ya bude account kuma sannu a hankali a cigaba da yin kasuwanci ta hanyar transfer, to ka ga sannu a hankali za toshe yin garkuwa da mutane domin biyan kudin fansa. Don ba ma kudin da za a basu.”

Masanin ya ce, hatta a kasar Amurka sun yi wani doka na cewa kada a biya kudin fansa ko sisi kan wani dan kasar da aka yi garkuwa da shi a wata kasa domin hana wa masu garkuwa da mutane samun kwarin guiwar cigaba da sheka ayarsu, “Muddin ba a biyansu kudin fansar nan to babu yadda za a yi su cigaba da yi.”

Farfesa Ahmed ya kara da cewa, “Madamar ana biyan kudin fansa to kamar ana gobara ne ana zuba fetur. Biyan kudin fansa ba magani ba ne, ya kara fadada abun ne. Don haka idan aka samar da wani yanayin da za a hana mutane biyan kudin fansa to za a samu nasara wajen dakile garkuwa da mutane.”

“Sannan idan zuwa kasuwanninmu musamman na sati-sati za ka ga yadda jama’a suke yawo da kudade. A zauna a sayi shanu a yi ta kirga kudade wani ya ce basu cika ba wani ya ce sun cika, ka ga inda transfer ne babu wannan matsalar balle ma a bata lokacin. Bugu da kari barayi su na kallo. Don haka in transfer ne za a samu saukin yin cinikayya.”

Ya ce, babbar matsalar da aka samu a Nijeriya shi ne ba a shirya wa sauyin ba aka dukufa wajen tilasta wa mutane, “kamata ya yi kafin a bijiro da wannan an kai kudade sosai a bankuna daga mutum ya je sai iya karba.

To amma kuma idan aka yi kudade sosai za a iya komawa gidan jiya. Domin idan mutum na da Miliyan goma kuma zai iya karba a lokacin da yake so zai karba ne ya je ya ajiye a gida, to ka ga dole a nemo hanyoyin da za a rage yawan kudaden da mutum zai iya karba domin a tabbatar mutane ba su ajiye kudade a gidajensu ba. Masu dan kananan hidimar kudi su na da damar amsar wani kaso na kudade domin tafiyar da harkokin yau da gobe.

“Masu kananan sana’o’i bai kamata a tauye su ba. An bai wa mutane dama su karbi 100,000 har sau biyar a sati, ka ga dubu 500,000, ka ga sun ma yi yawa. Mutum nawa ne suke amsar albashin 500,000 a wata? Ka ga ba su da yawa.

Ko 20,000 aka ce mutum ya karba a rana ya isheshi harkokin rayuwarsa na rana, mutum zai sayi kayan Miya, Achaba dole a basu kudi ba transfer ba, haka masu sadaka.

“Ka ga ba a yi shiri ba aka tilasta wa mutane. A kauyuka yawancin mutane ba su da account, kuma ga shi komai ya tsaya cak, ka ga sai ya zama kudurorin da ake son cimmawa sai ya zama ba su yiyu domin mutane ba su da account sai ya zama tsarin ya jefa mutane cikin wahala a kauyuka da karkara sai ya zama abun bai yi tasiri sosai ba. Amma da ya zama an fadakar da mutane muhimmanci yin account da hakan zai taimaka sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here