Shugabannin LP na kudu maso yamma sun yi wa Tinubu mubayi’a sun rungumi tsarin tafiyar APC

0
55

Makonni biyu gabanin zaben shugaban kasa, jam’iyyar Labour a shiyyar Kudu-maso-Yamma ta ruguje dukkan tsarinta na yankin zuwa jam’iyyar APC.

Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Da yake zantawa da manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar Litinin din da ta gabata, shugaban jam’iyyar LP na Kudu maso Yamma, Mista Omotoso Banji, ya bayyana cewa, babban kodinetan Kudu-maso-Yamma na kasa na Asiwaju Tinubu ne ya jawo su tafiyar APC. Dr. Dayo Adeyeye, da sauran mambobin kungiyar.

Omotoso wanda ya jagoranci tsarin komawa jam’iyyar ya ce shugabannin jam’iyyar LP sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne saboda ba ta da karfin da za ta iya lashe zaben da ke tafe.

Ya ce, “A halin yanzu jam’iyyar Labour ta zama dandali na kowa ya tsaya takara, dandamali ne na tsayawa takarar wadanda suka gaza, ni ban san Peter Obi ba kuma ban damu da shi ba amma ina damuwa da wadanda suke yin takara wadanda ba inda zasu je.

“Saboda haka, mu shugabannin jam’iyyar Labour a shiyyar Kudu-maso-Yamma mun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne saboda jami’iyyar ba kwararrun mutane wadanda za su kawo cigaba kuma abin da suke nema shi ne kudi, ba su shirya yi wa Nijeriya hidima ba.

“Jam’iyyar Labour ba ta shirya yi wa Najeriya hidima ba, shi ya sa muka yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar zuwa APC. Na ruguza tsarin jam’iyyar a jihar Ekiti. Don haka, ban san yadda Obi zai iya zuwa yanzu ya ci zabe a nan Kudu-maso-Yamma ba.

“Mu ne ginshikan waccan jam’iyyar a yankin Kudu-maso-Yamma, kuma cikin ikon Allah Madaukakin Sarki mun ruguza tsarin LP a yau (Litinin) mun rungumi APC. Na yi mamakin jin ta bakin shugaban jam’iyyar LP, Akin Osuntokun. Ba mu san shi a jam’iyyar Labour ba, Akin Osuntokun yana wakiltar muradin kan sa ne kawai.”

Ko’odinetan kungiyar SWAGA 2023, Dokta Dayo Adeyeye, a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka, ya umurci su da sauran ‘yan jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Yamma da su koma rumfunan zabe daban-daban, su yi wa Tinubu aiki domin ya samu nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

“Tinubu mutum ne mai kishi, aiki da hangen nesa, wanda a shirye yake ya canza kasar nan kuma ko suna so ko ba sa so, Tinubu zai yi nasara,” in ji Adeyeye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here