INEC ta fitar da jerin rumfunan zabe 124 da ta soke

0
65

Kwana 10 kafin zaben shugaban kasa,  Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen rumfunan zabe 124 da ta soke.

INEC ta ce ta soke rumfunan zaben ne a wasu jihohi 15, saboda babu ko mutum daya da ke da rajista a cikinsu, don haka, ba za a yi zabe a nan ba a wannan karon.

Jerin sunayen rusassun rumfunan zaben da INEC ta fitar ya nuna Jihar Imo ce a kan gaba da rumfunan zabe 38 da ka soke.

Ga jerin jihohin da abin ya shafa da kuma yawan rumfunan zabensu da INEC ta soke:

  1. Imo – 38
  2. Abia – 12
  3. Borno – 12
  4. Binuwai – 10
  5. Kano – 10
  6. Kaduna – 8
  7. Anambra – 6
  8. Bauchi – 6
  9. Adamawa – 4
  10. Delta – 4
  11. Ebonyi – 4
  12. Enugu – 4
  13. Jigawa – 3
  14. Bayelsa – 2
  15. Edo – 1.

A ranar 25 ga watan Fabrairu da muke ciki ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa na da Majalisun Tarayya, wanda bayansa da mako biyu za a gudanar da na gwamnoni da Majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here