An kori sanotoci 2 mata daga majalissa saboda tufafin da suka saka

0
33

Majalisar dattawan Kenya ta umarci sanatoci mata guda biyu da su fice daga zauren majalisar, saboda tufafin da suka sanya a lokacin da suka halarci zaman majalisar.

Ɗaya daga cikinsu ta saka riga marar hannu, ɗayar kuma saboda ganin ɗigon jini a wandonta kasancewar tana al’ada.

Sanata Gloria Orwoba ta shaida wa shugaban majalisar cewa lamarin jinin al’ada abu ne da ke aukuwa ga mata ba tare da sun shirya masa ba.

To amma an umarce ta da ficewa daga majalisar kasancewar ba a amince da ganin ɗingon jini a tufafi ba, dan haka dole ta sauya tufafi.

An kuma umarci takwararta Sanata Karen Nyamu da ta fice daga zauren majalisar sakamakon sanya riga marar hannu.

Sanatocin ɓangaren adawa sun yi ƙorafin cewa Ms Nyamu ta sanya tufafin da zai kawo rashin kunya a majalisar.

Shugaban Majalisar ya ce hakan saɓa wa dokar sanya tufafi ce ta majalisar, wadda ta tanadi cewa dole mata su sanya tufafin da za su kare mutuncinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here