Zanga-zangar sauya kudi: Gwamnan Kwara ya dakatar da taron yakin neman zabe a jihar

0
27

A ci gaba da nuna goyon baya ga al’umar jihar Kwara kan matsalolin da musanyar kudi ya haifar.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya dakatar da taron gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

AbdulRazaq ya sanar da hakan a gidan rediyon jihar da ke Ilorin, babban birnin jihar a ranar Laraba.

“A bisa halin da jama’a ke ciki, na dakatar da tarukan jam’iyyar APC har sai wani lokaci,” in ji gwamnan.

A yayin da yake kira da a kwantar da hankula, AbdulRazaq ya shaida wa al’umar jihar cewa har yanzu dokar da kotun koli ta bayar na izinin zama ci gaba da karbar tsohon kudin.

Sakon gwamnan yana cewa: “Ya ku al’ummar Jihar Kwara:

“Ina jajanta muku bisa yadda ake ci gaba da fama da karanci kudi sakamakon sake fasalin kudin da CBN ya yi a baya-bayan nan.

“ Kotun Koli ta ba da umarnin da zai ba da damar ci gaba da amfani da tsoho da sabbin takardun kudi tare. Wannan umarnin har yanzu yana nan har sai Kotun Koli ta yanke hukunci a kan haka.

“Saboda haka ina so ku kwantar da hankalinku, ku zama masu bin doka da oda da zaman lafiya, kada mu afka wa juna, ko mu lalata dukiyoyin juna.

“Ina kira gare ku da ku kwantar da hankalinku kada ku yi kasa a guiwa ko kuma ku shiga kowane irin tashin hankali.

“Ina shaida irin wahalar da wannan lamari ya haifar, ina mai tabbatar muku cewa wannan za a samu sauki nan da kankanin lokaci, ina matukar godiya da hakurinku.

“A don haka na dakatar da tarukan siyasa har sai zuwa wani lokaci nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here