Gwamna Zulum ya bada umarnin bada magani kyauta a asibitocin gwamnati saboda ‘karancin Naira

0
86

A jiya Laraba mai girma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin a saki magunguna da sauran kayayyakin jinya na sama da Naira miliyan 300 ga asibitocin gwamnati domin bayarwa ga marasa lafiya kyauta wadanda galibin su ke fuskantar matsala wajen biyan kudaden magani saboda karancin sabuwa da tsohuwar Naira.

Kamar yadda Komishinan lafiya Farfesa Mohammed Arab Alhaji, ya bayyana a lokacin da yake kaddamar da raba magungunan a runbum adana magani na ma’aikatar lafiya ​​da ke kan titin Baga a birnin Maiduguri.

Magungunan da aka rabar sun hadar na kare cuttuka, kayan karbar haihuwa da sauran su.

Komishinan lafiyar ya umurci manyan jami’an kiwon lafiya masu kula da cibiyoyin kula da lafiyar al’ummar da ke birnin Maiduguri da kewaye tare da ‘karamar hukumar Jere, da su gaggauta shirya duk wasu takardun da suka da ce domin karbar kason su cikin gaggawa.

Arab, ya jaddada cewa dole ne a ba da magungunan kyauta ga marasa lafiyar da ba su da kudi da kuma wadanda suka kasa samun kudaden su a banki domin biyan kudin magani.

Manyan jami’an kiwon lafiya na asibitocin gwamnati sun nuna jin dadin su ga wannan abun alherin da Gwamna Zulum ya yiwa al’ummar sa na bayar da magani kyauta ga mabukata, Dr Baba Shehu Mohammed, shine babban jami’i mai kula da asibitin Kwararru na Birnin Maiduguri a madadin sauran manyan jami’an asibitocin gwamnati ya mika godiyar sa ga gwamnan.

Baya ga haka komishinan lafiyan ya ce ma’aikatar sa za ta hada guiwa da hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Borno wacce itace ke da alhakin karbar kudaden da ake biya a asibitocin gwamnati da First Bank domin kara samar da na’urorin POS a asibitocin gwamnati domin saukakawa marasa lafiya hanyar biyan kudaden maganin su dana jinya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here