HomeLabaraiMutum hudu sun mutu a rikicin rashin Naira a Edo

Mutum hudu sun mutu a rikicin rashin Naira a Edo

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Rahotanni na cewa rikici ya barke a sassan kasar nan, yayin da jama’a ke shan wahala wajen neman takardun kudi a bankuna, abin da ya haifar da asarar rayukan mutane akalla hudu a jihar Edo, kamar yadda jaridar Thenation ta ruwaito.

Birane da dama daga kudancin kasar ne aka fi samun tarzoma saboda karancin takardun kudin, yayin da ‘yan kasar ke zargin bankuna da hana jama’a kudade.

An rufe bankuna, yayin da masu sana’ar motar haya suka dakatar da zirga-zirga a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

A Warri da ke jihar Delta, fusatattun mutane sun cinnawa bankuna wuta, inda haka abin ya kasance a jihar Edo.

Haka zalika, an samu barkewar tarzoma a birnin Ibadan, yayin da al’umma da dama ke cigaba da bayyana fushin su, saboda karancin takardiun kudin.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da kotun kolin kasar ta dage cigaba da ssauraron karar da wasu jihohi suka shigar gabanta, kan wa’adin ranar 10 ga watan fabrairu da CBN ta ayyana a matsayin ranar da zza a daina karbar tsoffin takardun kudi.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here