Emefiele: Rikita-rikitar gwamnan CBN

0
51

Kimanin shekara guda ke nan Gwamnan Babban Bankin Najeria (CBN), Godwin Emefiele, yana tayar da kura da kasar.

Emefiele, shi ne kusan shi ne jami’i tilo mafi girman matsayyi da gwamnatin Shugaban Buhari ta APC ta gaje shi daga tsohuwar Gwamnatin Shugaban Goodluck Jonathan ta PDP kuma take damawa da shi, yake kuma jawo ce-ce-ku-ce.

Yanzu kusan shekara guda ke nan da ake ce-ce-ku-ce kan Emefiele, musamman tun bayan da ya rikide ya koma dan siyasa tare da neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, a zaben dan takarar da ya gudana a watan Mayun 2022.

Neman takarar shugaban kasa

Sayen fom din neman takarar da ya yi a kan Naira miliyan 100 ya jawo surutai, amma ya ce ba daga aljihunsa ya sayi fom din ba, wasu masu kaunar sa ne suka saya suka ba shi domin ya nemi takarar jagorancin Najeriya.

Tun kafin nan, an yi ta ji-ta-ji-tar cewa zai fito neman takarar, amma ya karyata, daga baya da ta tabbata, sai ake suka nemi ya yi murabus daga mukaminsa na CBN, tun da ya zama dan siyasa.

Amma shi da bankin suka ce allambaram, hakan ba zai shafi aiki ko kimar bankin ba, har ma ya je kotu, kuma ta sahale masa tsayawa takara, amma APC, Bola Ahmed Tinubu ya kayar da shi.

Bayan zaben dan takara da ya fadi, ya dawo ya ci gaba da aikinsa a CBN, wanda shi ma ya kawo ce-ce-kuce da kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa, tunda ya zama dan siyasa, amma hakar masu surutan ba ta cim ma ruwa ba.

Zargin ta’addanci

A gefe guda kuma Hukumar tsaro ta DSS tana bincike a kan Mista Godwin Emefiele domin gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin almundahana da daukar nauyin ta’addanci.

Zarge-zargen, kamar yadda kafar yada labarai ta Premium Times ta bayyana a takardar kotun da ta samu, sun hada da daukar nauyin ’yan bindiga da kungiyar ta’addanci ta IPOB, zagon kasa ga Gwamnatin Buhari da kuma wasu abubuwa da ke barazana ga tsaron Najeriya.

Bugu da kari, ana zargin sa da damfara, karkatar da kudaden Bankin NIRSAL da na shirin tallafin noma na Anchor Borrower wadanda duk suke karkashin kulawar CBN.

Wasu rahotanni dai na zargin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da bai wa Emefiele kariya a gida da kuma ofishinsa, domin hana a kama shi, zargin da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta.

Daukar nauyin IPOB

Ana zargin Gwmanan na CBN ne da daukar nauyin reshen soji na kungiyar IPOB, wato ESN, ta hanyar amfani da kudaden sata da kuma ragowar wadanda ya yi amfani da su wajen neman takarar shugaban kasa.

IPOB dai kungiya ce da ke neman ballewa daga Najeriya, kuma ta dade tana kai miyagun hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati tare da kashe mutane, musamman jami’an tsaro.

Maharan sun kashe fararen hula da dama, tare da tilasta wa mazauna yankunan Kudu maso Gabashin Najeriya zaman gida a ranakun Litinin.

A baya-bayan nan dai IPOB ta tsananta kai hare-hare a kan ofisoshin ’yan sanda, inda take kashe jami’ai ta sace makamai, sai kuma ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), inda suke kona kayayyakin zabe.

Dambarwar sauyin kudi

Tun a lokacin da Emefiele ya sanar da shirin CBN na sauyin takardun Naira 200, 500 da 1,000 da kuma tsarin takaita amfani da tsabar kudi Emefiele ya sake dawowa bakin ’yan Najeriya.

A kwanakin baya, dan Majalisar Wakilai, Honorabul Muhmmed Gudaji Kazaure ya zargi Emefiele da karkatar da wasu kudade da yawansu ya kai Naira tiriliyan 89 na kudin harajin kan sarki.

Wannan zargi dai ya yamutsa hazo, amma Emefiele ya yi fatali da shi a matsayin na kanzon kurege.

A gefe guda kuma Gudaj ya dage cewa a shirye yake su hadu a kotu, domin kuwa yana da kwararan hujjoji cewa an karkatar da kudaden,

Ya kuma zargi gwamnan CBN din da miyagun tsare-tsaren kudi domin azurta kansa da mukarrabansa.

Dambarwar sauyin kudi

Tun farkon bullo da batun sauyin kudi aka sa zare tsakanin CBN da Ministar Kudi da Tsare-tsare, wadda ta ce ma’aikatarta ba ta da masaniya a kan lamarin.

Ta kuma yi gargadi cewa matakin zai kawo matsalar tattalin arziki kuma yana da hadari ga darajar Naira.

Sai dai Mista Emefiele ya ce, sauyin kudin doka ce, kuma za a yi ne domin karya tattalin arzikin ’yan ta’adda da ke karbar miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa.

Sauran dalilan sun hada da rage hauhawar farashin kaya, yaki da almundahana, farfado da darajar Naira da kuma dakile masalar masu buga jabun takardun kudin da kuma rage awan sabar kudaden da ke hannun jama’a.

A gefe guda kuma Gudaji Kazaure ya zargi gwamnan CBN din da amfani da sauyin kudin domin huce haushinsa kan faduwarsa a zaben dan akarar shugaban kasa na APC da aka kayar da shi.

’Yan Najeriya sun yi ta korafi kan batun, lamarin da ya sa Majalisa ta bukaci Emefiele ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.

Sau biyu majalisa na gayyatar sa ba tare da ya hallara.

Da farko ya aike wa kwamitin majalisar cewa ya yi tafiya kasar waje domin aiki, wanda ya sa aka dage zaman, inda a karo na biyu ya turo wakiliyarsa bisa uzurin cewa yana duba lafiyarsa a kasar waje.

Sai daga bisani, ya dawo suka gana, kurar ta dan lafa, amma duk da haka ’yan majalisar ba su yarda ba, inda suka bukaci karin lokacin sauyin kudin.

Babu labari mai dadi

Ana gab da cikar wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kudin da aka sauya, aka yi ta ji-ta-ji-tar cewa za a kara lokaci.

Ana tsaka da haka ne Emefiele, bayan wata ganawa da ya yi da Buhari, ya sanar cewa ba za a kara lokacin ba.

Bayan an yi ta kai ruwa rana, a ranar 30 ga watan Janairu, Emefiele ya sanar cewa Shugaba Buhari ya kara wa’adin da kwana 10, zuwa 10 ga watan Fabrairu.

Idan mai karatu zai tuna, tun a jajibirin fara aikin dokar sabbin takardun kudin suka gagari ’yan Najeriya samu, sai sun je banki, ga shi kuma sabbin kudin ba sa samuwa.

Lamarin da ha haifar dogayen layuka da guna-guni daga ’yan Najeriya, musamman ganin cewa a wasu bankunan, abin ake ba su bai wuce N3,000 ba na sabbin kudin.

Kotun Koli

Bayan cikar wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu, da rashin nasarar gwamnonin APC wajen ganin Shugaba Buhari ya kara wa’adin, wasu daga cikinsu suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli suna neman ta dakatar da haramcin tsoffin takardun kudin.

Kotun ta ba da umarnin wucin gadi bisa bukatar gwamnonin sannan ta dage zaman.

Gwamnonin sun dauki matakin ne bayan Buhari ya ce su ba shi kwana bakwai zai yi tunani, yana mai jaddada cewa CBN ya ba shi tabbacin zai wadatar da ’yan kasa da sabbin kudaden.

Daga bisani Majalisar Koli ta Kasa ta yi zaman inda ta gayyaci Emefiele, ta umarci CBN ya samar da sabbin takardun kudin a wadace, ko kuma a ci gaba da amfani da tsoffin.

Bayan nan ne Koun Koli ta umarci jihohi 12 da suka shigar da kara gabanta su hade karar a wuri daya da kuma bangaren da ake kara a gefe guda, sannan a dage sharia’r zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu.

CBN ya lashe amansa

Daga bisani ne Buhari ya ba da umarnin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, tsohuwar N500 da N1,000 sun daina aiki, amma masu su na iya kaiwa CBN a tura zuwa asusun bankinsu.

Washe garin fara hakan, bayan ’yan Najeriya sun yi cikar kwari a rassan CBN da ke jihohi, babban bankin ya fitar da sanarwa cewa masu tsoffin kudin da ba su wuce N500,000 ba su kai wa bankunan kasuwanci, wadanda ke da sama da N500,000 kuma su kai ofisoshinsa.

Cikin dan lokaci bayan fitar sanarwar da CBN ya aike wa bankunan kasuwanci, ya lashe amansa, yana mai karyata sanarwarsa ta farko.

Duk da haka a halin da ake ciki, wasu bankunan kasuwanci sun ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin daga hannun jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here