Jamb ta dakatar da rijistar DE ta 2023

0
87
  1. Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta dakatar da gudanar da rijistar shiga kai tsaye ta shekarar 2023, wanda aka fara a ranar litinin, 20 ga watan Fabrairu, 2023.

Dakatar dai, a cewar wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a da kuma ka’idojin hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar a ranar talata, domin a samu damar aiwatar da wasu matakai, wadanda aka tsara don kyautatawa masu son rijistar.

Ya ce, “Saboda haka, Hukumar ta bayyana cewa, sabon kwanan wata da sabbin hanyoyin rajistar, wadanda za su hada da Upload na Admission Letter na JAMB a sha’anin OND da NCE, da takardar shaidar shiga jami’o’i dangane da takardar shaidar kammala Jami’a, da kuma takardar shiga jami’o’i. ta hukumomin jarrabawar A’ Level (IJMBE, JUPEB, da dai sauransu), za a sanar da su nan gaba kadan domin daliban su zarce ofisoshin JAMB a fadin kasar domin yin rajista.”

Idan dai ba a manta ba Hukumar ta fara rajistar DE ne a ranar Litinin 20 ga Fabrairu, 2023, kuma ta tsayar da ranar alhamis 20 ga Afrilu, 2023.

Haka kuma daliban su lura cewa ofisoshin JAMB ne kadai aka amince da su yi rajistar DE.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here