‘Yan Najeriya miliyan 87.2 ne za su tantance makomar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Peter Obi yayin da INEC ta fitar da bayanan karshe na zaben 2023

0
55

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa masu kada kuri’a 87,209,007 ne za su tantance wanda zai zama shugaban Najeriya a tsakanin Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na Jam’iyyar Labour, da Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da sauran su.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023, yayin wani taron manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa da ke Abuja.

Dukkanin jihohin uku sun ci gaba da zama bisa ga tsarinsu na farko dangane da adadin PVC da jihohi suke dashi inda suka rike kanbunsu na jahohi mafiya yawan kuri’a.

Jimlar adadin PVCs da ba a tara ba ya tsaya a 6,259,229 (6.7%) har zuwa 5 ga Fabrairu, 2023.

A cewarsa, daga cikin masu kada kuri’a miliyan 93,469,008 a kasar, 87,209, 007 sun karbi katin zabe na dindindin (PVCs) kuma za a ba su damar kada kuri’a a zaben shugaban kasa na ranar Asabar.

Yakubu ya sanya adadin sabbin PVCs da aka tattara bayan kammala rajistar masu kada kuri’a (VCR) na karshe da kashi 93.3%.

Wani rahoto daga Jihohi da aka tattara na PVC ya nuna cewa Legas ce ke kan gaba da katunan zabe 6,214,970, Kano na da 5,594,193 yayin da PVC na Kaduna ya kai 4,164, 475.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here