Atiku ya lashe Bauchi, ya kada Tinubu, Kwankwaso da Obi

0
25

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a Kananan Hukumomi 18 cikin 20 na Jihar Bauchi.

Jami’in tattara sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Bauchi, Farfesa Abdulkarim Sambo, wanda shi ne mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutse ne, ya bayyana sakamakon zaben.

Sambo, ya ce Atiku ya samu kuri’u 426,607, inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 316,694 wanda ya lashe kananan hukumomi biyu kacal da suka hada da Toro da Gadau.

Dan takarar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya zo na uku, inda ya samu kuri’u 72,103, yayin da dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya samu kuri’u 27,373.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here