Yin tattaki a kullum na rage haɗarin mutuwa da wuri – Bincike

0
90

Ba wai sai ka kasance ɗan tsere ba ko kuma mai harkar wasu wasanni ba domin cin moriyar alfanun motsa jiki – soma yin tattaki a kowace rana ya wadatar, kamar yadda wani nazari da aka yi a Birtaniya ya nuna.

Nazarin ya gano cewa idan mutum zai yi tattaki na aƙalla minti 11 a kowace rana, hakan na iya rage haɗarin mutuwar wuri ta mutum ɗaya cikin 10.

Akasarin mutane ba sa iya samun damar motsa jiki duk mako na tsawon minti 150 da aka bayar da shawara.

Amma ko ba komai gara a ce mutum yana motsa jikinsa maimakon a ce ba ya yin komai, in ji masu binciken daga Jami’ar Cambridge.

Hukumar Lafiya ta Birtaniya, NHS ta bayar da shawarar kowane mutum ya riƙa motsa jiki na tsawon minti 150 zuwa 300.

Wanda a cewarta hakan zai ƙara bunƙasa lafiyar zuciya kowane mako.

Ko kuma motsa jiki tuƙuru na tsawon minti 75 zuwa 150 a kowane mako, wanda hakan ke ƙara lafiyar zuciya ta hanyar inganta numfashi.

Tawagar masu binciken ta duba wasu nazarce-nazarce da aka yi a baya game da alfanun motsa jiki.

Bisa wannan binciken ne ta yanke shawarar cewa yin rabin abin da aka bayar da shawara, na iya kare mutum ɗaya cikin ashirin daga cututtukan zuciya da kuma kusan mutum ɗaya cikin 30 masu fama da cutar daji.

Hakan ya yi dai-dai da minti 75 a kowane mako – ko kuma minti 11 a kullum – tuƙa keke da yin tafiya da sauri ko hawa tsauni ko rawa ko kuma yin wasan ƙwallon tennis”

Dr Soren Brage, wanda ya jagoranci binciken ya ce “ya kamata ku ji jikinku na motsi, zuciyarku na bugawa da sauri amma ba lalle ku ji numfashinku ya ɗauke ba.”

Yin hakan daidai yake da rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar ɓarin jiki da kashi 17 cikin 100 da kuma cutar daji da kashi bakwai cikin 100, kamar yadda binciken ya nuna.

Motsa jiki a kai-a kai yana rage yawan kitse a jiki da kuma ƙara yawan jini yayin da kuma yake inganta lafiyar jiki da bacci da na zuciya na tsawon lokaci.

Amfanin motsa jiki ya fi yawa ga wasu nau’ukan cutar daji kamar ta kai da wuya da ciki da wadda ke haddasa ƙarancin jini (leukaemia) amma amfanin motsa jikin ba shi da yawa ga cutar dajin da ta shafi huhu da hanta da kansar mama.

Ba kowa ba ne yake jin sauƙin motsa jikin da hukumar lafiya ta Birtaniya (NHS) ta bayar da shawara a riƙa yi ba – mutane biyu cikin uku sun ce suna motsa jiki na ƙasa da minti 150 (sa’a biyu da rabi).

“Idan ka kasance wanda yake ganin motsa jiki na tsawon minti 150 duk mako a matsayin abu mai wahalar gaske, to bincikenmu zai kasance labari da zai faranta maka rai,” in ji Dr Brage.

“Idan kuma kana ganin za ka iya yin minti 75 kana motsa jiki, toh za ka iya duba yiwuwar tsawaita lokacin a hankali har zuwa yin yawan mintunan da aka bayar da shawarar yi.”

Nazarin da aka wallafa a mujallar British Journal of Sports Medicine, ya duba sauran binciken da aka wallafa kan amfanin motsa jiki a kusan manyan bincike 100 da kusan 200 da aka sake nazarinsu domin bayyana hujjojin binciken.

Masu nazarin sun kammala da cewa, idan kowane mutum zai iya tattaki na minti 150 a mako guda – to hakan zai iya kare mutuwar da ake samu ta wuri akalla ta mutum ɗaya cikin shida.

Masu binciken sun ce abin da ake buƙata shi ne mutane da daina wasu ɗabi’un kawai.

Misali, idan mutum zai je kanti siyayya sai ya taka da ƙafa ko kuma ya hau keke maimakon ya hau mota.

Ko kuma idan kana wasa da ‘ya’ya ko jikokinka ka zama mai kazar-kazar sosai.

Ka sa wasu abubuwa da kake jin daɗin yinsu a cikin abubuwan da ka saba yi a duk mako, wannan na daga hanyar da za ka riƙa motsa jikinka da kyau, a cewar masannan.

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta shawarci manya su riƙa yin abubuwan da za su riƙa motsa gaɓoɓinsu sau biyu a mako.

Misali wasan Yoga ko na motsa gaɓoɓi da jijiyoyin jiki kamar wasan lanƙwasa ko ɗaga wani abu mai nauyi ko aikin lambu ko tafiya da jaka mai nauyi, duka waɗannan suna da amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here