DA DUMI-DUMI: Kotun koli ta ba da umarnin ci gaba da kashe tsofaffin kuɗi a Nageria

0
81

A ranar Juma’a ne kotun kolin kasar nan ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500, N1,000 har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

 Kotun kolin ta kuma soke dokar da gwamnatin tarayya ta yi na sake fasalin kudin Naira, inda ta bayyana hakan a matsayin cin fuska ga kundin tsarin mulkin Nigeria wanda akai masa gyara 1999.

 Kotun koli ta yanke hukunci a karar da aka shigar da gwamnatin tarayya kan manufar sake fasalin kudin Naira.

 karar da jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka fara shigarwa kamfin daga bisani wasu jihohin su bi sahunsu wajen kalubalantar kadatar da amfani da kudaden tun a 31 ga watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here