Zaben 2023 shi ne mafi muni a tarihin Najeriya – Atiku

0
45

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar kuma ‘dan takarar zaben shugaban kasar da akayi a kasar a karkashin Jam’iyyar PDP, yace zai je kotu domin neman soke da zaben da akayi a karshen mako saboda kura kuran da aka tafka.

Atiku wanda ya bayyana zaben a matsayin mafi muni a tarihin dimokiradiyar Najeriya ya zargi hukumar zabe da kin mutunta dokokin zaben da aka samar abinda ya kaiga bada damar tafka magudi da kuma kin amfani da na’urar zamani wajen aikewa da sakamako.

‘Dan takarar yace bayan ganawa da kuma tuntubar jiga jigan jam’iyyarsu ta PDP sun yanke hukuncin zuwa kotu domin gabatar da hujjojin da suke da shi domin ganin an soke zaben.

Ya kuma kara da cewa bai san dalilin da ya sa shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu ke saurin gabatar da sakamakon zaben da akayi ba, duk da korafe korafen da aka gabatar wadanda ya dace ace ya duba su domin yin gyara.

Atiku ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarin da ya dauka na tabbatar da ganin an samu karbabben zaben da ya dade yana alkawari domin baiwa jama’a damar zabin abinda suke so.

‘Dan takaran ya kuma bukaci alkalai da bangare shari’a da suyi abinda ya dace domin wanke kansu wajen bada hukuncin da ya dace da abinda ‘yan Najeriya ke so.

Atiku yace ya dade yana kalubalantar rashin adalci da kuma tabbatar da dimokiradiya a Najeriya abinda ya sa ya kai mai gidansa shugaba Olusegun Obasanjo kotu har sau 11 kuma yana samun nasara akansa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace bai taba zuwa ya ga wani alkali a bayan fage ba domin ganin an taimaka masa, abinda ya sa yake yabawa bangaren shari’ar saboda rawar da yake takawa na tabbatar da adalci a kasar.

Dangane da hukuncin da kotun koli zata yanke, Atiku yace idan bai samu nasara ba, zai mayar da al’amarinsa ga Ubangiji saboda itace matakin karshe na nemab hakki kamar yadda dokokin kasa suka tanada.

Atiku Abubakar na bayyana hakan ne, a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, babban birnin kasar.

Tun farko babbar jam’iyya hamayya ta PDP ta bukaci INEC da ta gaggauta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Tinubu tare da soke zaben, sakamakon zargin ta saba wa sashe na 65 na dokar zabe ta 2022.

A cewar jam’iyyar, INEC ta sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, da dokar zabe ta 2022 da kuma ka’idojin INEC na gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.

Sanarwar da PDP ta fitar a ranar Alhamis, ta ce dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, a fili ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, bayan da ya samu rinjayen kuri’un da ‘yan Najeriya suka kada a rumfunan zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here