Dalilin da ya sa Juventus ta dakatar da Pogba

0
98

Juventus ta yi wasa ba tare da dan wasan tsakiyarta Paul Pogba ba, a nasarar da ta samu a kan Freighburg a zagayen kungiyoyi 16 na gasar Europa a daren Alhamis.

Wata majiya daga kungiyar ta ce an yanke  shawarar yin wannan wasa ba tare da Pogba bane saboda dalilai na rashin da’a.

Dan wasan tsakiyar na Faransa bai buga kusan dukkannin wasannin wannan kaka ba saboda rauni da yake jinya, kuma ba a sanya shi a cikin jerin ‘yan wasan da suka fafata a daren Alhamis ba.

Majiyar ta ce kocin Juventus Massimiliano Allegri  ya dauki wannan mataki ne sakamakon  Makara da dan wasan mai shekaru 29 ya yi na zuwa wani taron da tawagar ta yi a yammacin Laraba.

A makon da ya gabata ne Pogba ya buga wa Juventus wasan farko tun da ya yi mata kome daga Manchester United a kakar da ta gabata, kuma ya shigo ne bayan  hutun rabin lokaci a wasan da suka yi nasara a kan Torino a ranar Lahadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here