Ba da izini na CBN ya ƙi bin umarnin kotu kan takardun ƙudi ba – Buhari

0
115

Fadar shugaban Najeriya ta ce Babban Bankin ƙasar ba shi da wani dalili na ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli kan sabbin takardun kuɗi don fakewa da sunan jiran umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa inda ya ce Shugaban ƙasar bai umarci atoni janar na ƙasa, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emiefele su ƙi martaba umarnin kotu ba da ya shafi gwamnati da wasu ɓangarorin.

A ranar 3 ga watan Maris ne Kotun ƙolin ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun ƙudi har zuwa 31 ga watan Disamban bana.

Umarnin kuma ya zo ne bayan da gwamnonin jihohi 16 suka ƙalubalanci matakin sauya fasalin kuɗin.

Jihohi 16 ƙarƙashin jagorancin Kaduna da Kogi da Zamfara sun buƙaci kotun ƙolin ta soke matakin gwamnatin bisa dalilan cewa hakan ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da wahala.

Kotun ta ƙara da cewa rashin martaba umarnin kotun na ranar 8 ga watan Fabrairu, alama ce ta mulkin kama-karya inda ta bayyana cewa shugaban ya saɓa wa Kundin tsarin mulkin ƙasa a yadda ya bai wa CBN umarnin sake fasalta kuɗin ƙasar.

Sanarwar dai ta ce Shugaban ƙasar babban mai mutunta dokoki ne kuma babu adalci a yadda ake yi sukar Shugaban da yi masa mummunan zato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here