Pogba zai sake yin jinyar makwanni 3

0
50

Dan wasan  tsakiya na Juventus, Paul Pogba zai koma wata jinyar, bayan da ya raunata kafarsa a  yayin da yake daukar bugun tazara.

Pogba mai shekaru 29 zai  yi jinyar kusan makowanni 3, saboda haka ba zai samu fafatawa a wasan neman tikitin zuwa gasar Euro 2024 da kasarsa Faransa za ta fara ba.

Bayan da aka yi wasa babu shi saboda dalilai na rashin da’a a karawar  Juventus da Frighburg a wasan gasar Europa League a makon da ya gabata, Pogba bai buga wasan  da Juventus ta lallasa Sampdoria da ci da  2  da 0 ba.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar  ta ce an yi wa Pogba gwaje-gwaje a ranar Litinin, inda aka tabbatar da ya samu matsalar cirar tsoka a cinyarsa.

Juventus za ta koma filin fafatawa a gasar Europa ranar Alhamis na wannan makon  ba tare da Pogba ba a wannan karon sakamakon rauni.

Sau biyu kawai ne Pogba ya buga wa Juventus wasa a matsayin canji tun da ya yi mata kome daga  Manchester United a kakar da ta wuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here