Yan sanda sun kama magidanta 3 bisa zargin lalata da kananan yara a Gombe

0
54

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu magidanta uku bisa zarginsu da yin lalata da kananan yara mazauna unguwar Kagarawal fyade a lokuta daban-daban.

An kama magidantan ne masu suna Sani Adamu mai shekara 50 da ke zaune a unguwar Kagarawal da Adamu Muhammad mai shekara  40 da shi ma yake zaune a unguwar Malam Inna sai kuma Bakura Muhammad mai shekara 30 shi a Malam Inna bisa zarginsu da yi wa wasu yara uku.

Yaran dai ‘ya’yan Malam Aliyu Adamu ne da ke zaune a unguwar ta Kagarawal a Gombe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya bayyana hakan ta cikin wata takarda da ya aike wa manema labarai a madadin Kwamishinan ‘yan sanda Oqua Etim.

Ya ce a ranar 7 ga watan Maris wasu mutum biyu masu suna Aliyu Adamu da Alhaji Abba da ke kungiyar kare hakkin dan adam ne suka kai korafi ofishin ‘yan sanda na shiyyar Gombe cewa suna zargin wadannan mutane uku da yi wa yaran da aka sakaya sunayensu fyade.

A cewar ASP Mahid, mutanen sun ce daga watan Janairu zuwa Maris na 2023, a lokuta daban-daban wadannan mutane sun yi wa yaran fyade a wurare mabanbanta a unguwar ta Kagarawal ba tare da son ransu ba.

Yace an kai yara da kuma mutanen da ake zargi zuwa Asibitin ‘Yan Sanda wato Police Clinic don yi musu gwaji.
Sai dai ya ce a asbitin ne duka magidantan suka amsa laifin cewa tabbas suna lalata da yaran.

Sai dai ya ce a asbitin ne duka magidantan suka amsa laifin cewa tabbas suna lalata da yaran.

Mahid ya ce yanzu dai suna ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su tura wadanda ake zargin zuwa kotu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here