AbdulRazaq na APC ya samu wa’adi na biyu a Kwara

0
44

.

Hukumar zabe a jihar Kwara ta sanar da AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar.

Hakan na nufin ya samu wa’adin mulki na biyu kenan.

AbdulRazaq na jam’iyyar APC ya doke Alhaji Shuaib Yaman Abdullahi na jami’yyar PDP da kuma Alhaji Hakeem Oladimeji Lawal na SDP.

Babbar jami’in da ke lura da zaben watau Farfesa Isaac Itodo ya bayyana cewa gwamnan ya samu nasara a duka kananan hukumomi 16 na fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here