An kashe ‘yan sanda 2, da dama sun raunata a wata arangama da sojoji a Taraba

0
42

A ranar Litin ne wasu sojoji suka kashe ‘yansanda biyu a jihar Taraba.

An harbe su ne da safiyar Litinin a garin Jalingo, wasu kuma sun tsira da harbin bindiga inda a yanzu ake duba lafiyarsu a wani asibiti.

An rahoto cewa, lamarin ya afku ne biyo bayan wata arangama da suka yi da sojoji.

Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar, SP Abdullahi Usman ya sanar da cewa, lamarin ya faru ne yayin da wani soja da ke binciken ababen hawa a wani titi da ke daura da Hedikwatar INEC da ke Jalingo, ya tare wata jami’ar ‘yansanda da ke aiki a INEC don nemanta da ta bayyana masa kanta.

A cewarsa, daga nan sai sabani ya shiga a tsakaninsu inda jami’ar ta wuce zuwa cibiyar tattara sakamakon zaben, sojan kuma ya bita ya fitar da ita da karfin tuwo sai rikici ya kaure.

Kakakin ya kara da cewa, a yanzu kwamishina Yusuf A. Suleiman da kwamanda na bataliya ta shida  da ke Jalingo na kan tattaunawa kan lamarin inda suka amince da kafa kwamitin da zai yi bincike kan sabanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here