Gwamnatin tarayya ta amince da kashe sama da Naira miliyan dubu 4 don Gina Barikin Jami’an NDLEA

0
78

Majalisar zartaswa ta tarayya FEC, ta amince da kashe sama da naira biliyan hudu domin gina barikin jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

 

Da yake bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai bayan kammala taron FEC a ranar Laraba, babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce gina barikin ya zama dole sabida barazana da hare-haren da ake kaiwa ma’aikata da jami’an hukumar manya da kananansu.

“Abin da ofishin babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a ya gabatar a majalisar zartaswa ayau shi ne, bukatar gina barikin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA. Kamar yadda kuka sani, ana yawan samun kai hare-hare ga jami’an hukumar sabida dakile ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi.

“A cikin watanni uku na shekarar 2023, hukumar NDLEA ta kama kimanin mutane 18,940 da kwayoyi da aka kiyasta kudinsu ya haura Naira biliyan 40. Bugu da kari, an shigar da kararraki kan laifuka 2,904. Wadannan nasarorin da aka samu ba kokonto za a fuskanci barazanar da ba a taba gani ba a kan ma’aikata da jami’an hukumar.

 

“Sabida la’akari da wannan barazanar, Gwamnatin Tarayya ta amince da daukar matakan tsaro da a yanzu za su samar da kariyar da ake bukata ga jami’an hukumar” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here