Sankarau ya kashe yara 10, wasu 177 sun harbu a Najeriya

0
74

Kananan yara 10 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a Jihar Yobe, inda ake fargabar wasu 177 na dauke da kwayar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Doka Muhammad Lawan Gana, wanda ya je dubiyar wadanda suka kamu da cutar a asibiti, ya ce wata bakuwar kwayar cutar sankarau ce ta yi wannan barna a yankin Degubi na Karamar Hukumar Nangere ta jihar.

Dokta Gana ya ce gwamnatin jihar tana aiki haikan domin shawo kan cutar, inda take kokarin samo riga-kafin bakuwar kwayar cutar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar tana samar wa asibitoci magunguna da kuma gudanar da alluran riga-kafi da wayar da kan jama’ar yankin a game da illolin sankarau.

Gwamnatin jihar na kuma hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da sauran hukumomin duniya, domin shawo kan cutar.

Cutar sankarau wadda ke shafar kwakwalwa da laka, ta kasance babbar barazana ce ga lafiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here