‘Yan sanda sun kama direban mota da AK-47 guda 4 a Kano

0
87

Rundunar ‘yan sintiri ta Safer Highway sun kama bindigu kirar AK-47 guda hudu a wani sumame da suka kai a Kwanar Garko da ke karamar hukumar Garko a jihar Kano a kan hanyar Kano zuwa Bauchi.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, an kwato bindigogin ne a lokacin da rundunar ta kama wani direban motar safa da ke kokarin sauya alkibla yayin da daya daga cikin fasinjojin ya sauko rike da wani abin tuhuma.

“Bayan amsa da gaggawar da rundunar ta yi, sai mutumin da ke cikin motar ya jefar da kayan, ya tsere daga wurin, bayan bincike, an gano wanu buhu dauke da bindigogi kirar AK-47 guda hudu,” in ji shi.

Yayin da rundunar ta ke kara kaimi wajen kamo wadanda ake zargin, ta kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da kai rahoton faruwar al’amura, wadanda suka yi zargi zuwa ofishin ‘yansanda mafi kusa da su.

An umarci jama’a da su kira wadannan lambobin na kar-ta-kwana don bayar da rahoto; 08032419754, 08123821575, 0807609127 da 09029292926.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here