Home Addini Yaran Musulmai aka fi nuna wa kiyayya a Amurka – Rahoto

Yaran Musulmai aka fi nuna wa kiyayya a Amurka – Rahoto

0
66

Wani rahoto mai suna “Cigaba a tsaka da nuna bambanci” wanda Majalisar Musulman Amurka ta Council on American-Islamic Relations (CAIR), ya bayyana cewa yara Musulmai suna fuskantar kyara a Amurka.

CAIR dai ita ce kungiyar Musulmai mafi girma mai fafutukar kawo ‘yanci a Amurka. A rahoton nata, yara Musulmai suna fuskantar tsangwama da kuma nuna musu abubuwa nuna kiyayya ga Musulunci a makarantu.

Wannan nuna bambanci ya karu da kashi 63 a Amurka. Yara Musulmai sun gabatar da korafin lokutan da suka fuskanci kiyayya a makarantu saboda addininsu, duk da ayyukan nuna kiyayyar sun ragu.

Daraktan Bincike da Gogayya na CAIR, Corey Saylor ya ce “Tsangwama a makarantu da kuma amfani da abubuwan nuna kiyayyar Musulunci a cikin aji yana da ban tsoro. Duk da dai mun yi murnar ganin raguwar hakan daga gwamnati, amma yara sun zamo abin hara”.

Ya ba da misali da wani abu da ya faru a Oktoban 2022 ga wata daliba ‘yar Afghanistan da ke aji uku na karamar sakandire a makaranta a jihar Maryland.

Yarinyar ta fuskanci tsangwama lokacin da ta shiga bayi don gyara daurin dankwalinta.

Yayin da yarinyar ta yi kokarin tserewa daga masu kyararta, sai wani jami’in makaranta ya rufe mata kofa.

A wani misalin kuma, malamin makaranta a jihar Florida ya tunkari dalabai uku Musulmai yayin da suke salla, inda ya kusan take su. Kyamara ta dauki abin da ya faru kuma bidiyon ya yi ta yawo a intanet.

An jiyo malamin yana cewa, “Na yi Imani da Yesu, shi ya sa zan katse musu ibada”.

Akwai sauran rina a kaba

Baya ga fannin ilimi, akwai inda kuma ake ganin kiyayya ga Musulmai a Amurka, kamar fannin bankuna inda ake budewa ko rufe asusun ajiya bisa la’akari da addini. Kuma hakan yana kawo babban tarnaki ga Musulmai a harkokin cinikayya da kudi.

Wani binciken jin ra’ayi da aka gudanar a watan Maris karkashin Cibiyar Tsarin Zamantakewa da Fahimtar Juna, ya gano cewa cibiyoyin kudi suna kawo tarnaki ga kashi 27 na Musulmai a Amurka.

A ta bakin Mr Saylor, dokoki kamar na Patriot Act, wadda ta fara aiki a Amurka bayan harin 9/11, sun bai wa hukumomin leken asiri karfin da yake janyo nuna bambanci.

Amma abin bai yi muni ba. Duk da an samu muni a wasu wuraren, a jimlace an samu raguwar nuna kiyayya ga Musulmai a karon farko cikin shekara 30 tun shekarar 1995, inda ya ragu da kashi 23.

Ya kuma bayyana cewa an samu karin kashi 32 na nuna wariya ga Musulmai a jami’an tsaro da gwamnati a shekarun farko na mulkin Shugaba Donald Trump.

A fahimtarsa, Saylor yana ganin raguwar nuna kiyayya ga Musulmai a shekarar 2022 ba za ta rasa alaka da sauyin gwamnati ba a fadar mulkin Amurka.

Hakan nan, yayin da jami’an tsaro suka soma mai da hankali kan wadanda suka haddasa harin 6 ga Janairu, ana sa ran ganin raguwar sa ido da leken asiri kan Musulmai masu bin doka da oda daga jami’an tsaro.

Sai dai kuma har yanzu Amurkawa ba su rungumi Musulmai tsiraru a matsayin wani bangare na al’ummar kasar ba, in ji Mr Saylor.

Saylor ya kuma ce, “Kyawawan alamun da muka gani a 2022 ba sa nufin za mu daina sanya ido. Har yanzu akwai kiyayya kewaye da mu.

“Muna ganin yadda kiyayya ga Yahudawa da ‘yan Asiya take karuwa. Muna kuma ganin zaluncin da ake wa bakake da masu duhun fata.”

“Raguwar rahotanni game da kiyayya ga Musulmai wani kyakkyawan abu ne. Amma sai an cigaba da aiki, ba tsayawa za a yi ba.”

Daraktan na CAIR, ya yi kira ga al’ummar Musulman Amurka su cigaba da shiga harkokin jama’a don isar da bukatunsu, saboda sai ana shigar a kara kan rashin adalci, kuma ana kafa sabbin dokokin magance matsalolin tsirarun da ke cikin al’umma.

“Idan kuka yi shiru, mutane za su kai muku hari. Amma idan kuka tashi tsaye don kare kanku, za su nemi wasu hanyoyin kawar da muguntar da ke zukatansu” a fadar Saylor.

“Idan ba ka hau teburin tattaunawa ba, to za a manta da kai a ajandar taro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp