Korona ta sauka daga matakin babbar barazanar lafiya ta duniya

0
65

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cewa annobar korona yanzu ta daina zama annoba “mai buƙatar ɗaukin gaggawa a duniya”.

Sanarwar, wani muhimmin mataki ne a yunƙurin kawo ƙarshen annobar da ta gama duniya.

Sabon matakin kuma ya zo ne shekara uku bayan hukumar lafiya ta ayyana jan hankali mafi girma a kan ƙwayar cutar.

Jami’an hukumar lafiya sun ce mace-mace sanadin ƙwayar cutar korona sun ragu daga ƙololuwar da suka taɓa kai wa na mutum 100.000 a mako cikin watan Janairun 2021 zuwa adadin fiye da mutum 3,500 a ranar 24 ga watan Afrilu.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce annobar ta kashe aƙalla mutum miliyan bakwai.

‘Gagarumin fata’

Sai dai shugaban WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce haƙiƙanin alƙaluman mace-macen da “mai yiwuwa” korona ta haddasa sun kusa kai wa mutum miliyan 20 – kimanin ninki uku a kan ƙiyasin da hukumomi ke fitarwa.

Ya Kuma yi gargaɗin cewa ƙwayar cutar har yanzu babbar barazana ce.

“Jiya, Kwamitin kai Ɗaukin Gaggawa ya yi taro a karo na 15, kuma ya ba ni shawarar cewa, na yi shelar kawo ƙarshen annobar a matsayin larurar jama’a mai buƙatar ɗaukin gaggawa da ta damu duniya.

Na amince da shawarar.

Don haka cikin ɗumbin fata, nake ayyana annobar korona da cewa ta zo ƙarshe a matsayin wata cutar al’ummar duniya mai buƙatar ɗaukin gaggawa,” Dr Tedros ya ce.

Ya ƙara da cewa an yi nazari a kan shawarar cikin tsanaki tsawon lokaci, kuma an cimma shawarar ne bayan bin diddigin alƙaluma cikin tsanaki.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa cire matakin jan hankali mafi girma da aka yi wa annobar korona, ba ya nufin hatsarinta ya kau, a cewarsa ana iya dawo da matakin da aka ba ta annobar da ke buƙatar ɗaukin gaggawa idan al’amura suka canza.

Ya ƙara da cewa an yi nazarin shawarar cikin tsanaki tsawon lokaci kuma an cimma ta ne bayan bin diddigi alƙaluma cikin tsanaki

“Abu mafi muni da wata ƙasa za ta iya yi yanzu shi ne ta yi amfani da wannan labari a matsayin wani dalili na watsar da matakan kariya, ta rusa tsare-tsaren lafiya da ta tanada, ko kuma ta aika saƙo ga mutanenta cewa cutar korona ba abar damuwa ba ce,” in ji shi.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tun farko ta ayyana korona a matsayin larurar da ke buƙatar ɗaukin gaggawa da ta damu duniya a watan Janairun 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here