Zaben Najeriya na 2023: Za a soma shari’a kan zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara

0
73

A ranar Litinin din nan 8 ga watan Mayu ne za a soma shari’a kan karar da jam’iyyun adawa a Najeriya suka shigar kotu don kalubalantar zaben da aka yi wa Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar.

An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara inda ya samu kashi 37 na kuri’un da aka kada.

Dan takarar da ke biye masa shi ne Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kashi 29 yayin da dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi ya samu kashi 25.

Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu ‘yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.

Atiku ya bukaci kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta sa INEC ta gudanar da sabon zabe wanda shi da Tinubu za su fafata.

Ya ce idan ba haka ba, ya kamata kotu ta soke zaben gaba daya sannan a sake gudanar da zabe.

Atiku ya ce Tinubu bai samu yawan kuri’un da suka isa a ayyana shi a matsayin shugaban kasa ba kuma bai cacanci tsayawa takara ba lokacin da aka gudanar da zabe.

A gefe guda, Mr Peter Obi ya nemi kotun sauraren kararrakin zaben da ta soke zaben sannan INEC ta gudanar da sabo kuma kada ta bari Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da jam’iyyar APC su shiga zaben.

Kazalika dan takarar na LP yana so kotu ta bayyana cewa Tinubu bai lashe zaben da kuri’u mafi rinjaye ba.

Haka kuma ya bukaci kotu ta kwace takardar shaidar yin nasara a zabe da INEC ta bai wa Tinubu, sannan ta ba shi Obi sabuwar shaidar lashe zaben shugaban Nijeriya.

Peter Obi ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben kuma ita kanta INEC ta ki yin biyayya ga dokarta inda ta sanar da sakamakon zabe kafin a gama sanya shi a na’urar tattara sakamako.

A nasa bangaren, zababben shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya gaya wa kotun cewa Peter Obi bai cancanci kalubalantar nasararsa a zaben shugaban kasar ba.

Ya ce ba a bi ka’ida ba wajen tsayar da Mr Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na LP.

Ya kara da cewa Peter Obi ya sauya sheka daga PDP zuwa LP kasa da wata daya kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar.

Kazalika ya ce Atiku ba shi da hujjar da za ta sa a soke zabensa, yana mai bukatar kotun ta yi watsi da kararsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here