Najeriya ta rasa matsayinta na kasar da ta fi samar da danyen mai a Afirka

0
71

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton wata wata na watan Afrilu da kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai  ta fitar a karshen makon da ya gabata.

Najeriya ta yi asarar gangunan danyen mai dubu 270 a watan Maris, kamar yadda alkalumman kungiyar OPEC din suka nuna.

OPEC ta ce gaba daya, mamboninta 13 na samar da gangunan mai miliyan 28 da dubu 60  a kowace rana a cikin watan da aka yi la’akari  da shi wajen yin wannan rahoto.

Ta ce an samu karuwar danyen man da ake samarwa a Sudiyya, Angola da Iran, a yayin da aka samu akasin haka a Iraq da Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here