EFCC na binciken gwamnan Zamfara kan almundahanar biliyan 70

0
50

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta ce gwamnan Jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle na fuskantar bincike kan zargin almundahanar Naira biliyan 70.

Hukumar, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ana binciken gwamnan na APC kan zargin cin hanci da rashawa, bayar da kwangiloli da kuma karkatar da sama da Naira biliyan 70.

“Kudaden da aka samo a matsayin lamuni daga tsohon bankin da ake zargin don gudanar da ayyuka a fadin kananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ne ya karkatar da su ta hanyar wasu ‘yan kwangila wadanda suka karbi kudin kwangilar da ba a aiwatar da su ba.”

“Binciken da Hukumar ta gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa sama da kamfanoni 100 ne suka karbi kudaden, ba tare da wata shaida ta hidimar da aka yi wa jihar ba.”

EFCC ta ce an gayyaci wasu daga cikin ‘yan kwangilar tare da yi musu tambayoyi, inda ta kara da cewa “sun bayyana bayanai kan yadda ake zargin gwamnan ya tilasta musu mayar masa da kudaden da suka karba daga asusun gwamnati ta hannun mukarrabansa bayan sun mayar da su Dalar Amurka”

.“Sun tabbatar da cewa ba su yi wa jihar Zamfara wani aiki ba amma an ce an umarce su da su mayar da kudaden da aka biya su dalar Amurka su koma hannun gwamnan jihar ta hannun wasu kwamishinoninsa, musamman kwamishinonin da ke kula da harkokin kudi da kananan hukumomi.”

“A ci gaba da bincike kan bada kwangilar da gwamnatin Matawalle ke yi, musamman na ayyuka a kananan hukumomi, hukumar ta kwato kudi Naira miliyan 300 daga wani kamfani mai suna Fezel Nigeria Limited. An gano kudaden ne zuwa kamfanin Zamafara Investment Company.

“A Nijeriya gwamnoni da mataimakansu na da kariya daga fuskantar tuhuma yayin da suke kan mulki, dalilin da ya sa har yanzu EFCC ba ta kama Gwamna Matawalle ba ke nan.”

Matawalle, wanda ya sha kaye a zaben gwamnan jihar na 2023 a watan Maris, zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara hudu a ranar 29 ga wata Mayu, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here