EFCC ta kammala shirin kama wasu gwamnonin Najeriya

0
67

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC ta kaddamar da gagarumin bincike akan wasu gwamnonin kasar da mataimakansu dake shirin mika mulki a ranar litinin mai zuwa, sakamakon kawo karshen kariyar tuhumar da suke da ita kamar yadda doka ta tanada.

Wani bincike da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta gudanar, yace Hukumar EFCC ta baza komarta domin cafke wasu daga cikin gwamnonin da mataimakansu 28 dake shirin sallama da gidajen gwamnati a makon gobe.

Binciken yace tuni EFCC ta bukaci takardun kadarorin da wadannan gwamnoni suka cika kafin fara aiki, wanda ya bayyana irin dukiyar da suka mallaka a wancan lokaci, yayin da kuma take dakon wadanda zasu bayar ayanzu domin nazari akansu.

Jaridar tace hukumar tayi shiri tsaf domin ganin wadannan gwamnoni basu gudu sun bar kasar ba, bayan mika mulki ga wadanda zasu gaje su a ranar litinin mai zuwa.

Ko a makon jiya, shugaban hukumar Abdurasheed Bawa, ya dada jaddada shirin EFCC na bin diddigin wadannan gwamnoni da mataimakansu dake shirin sauka, sakamakon korafe korafe da kuma zarge zargen da ake musu da rub da ciki da kudaden talakawa.

Daga cikin gwamnonin da Bawa ya bayyana, akwai na Jihar Zamfara, Bello Matawalle wanda yace ana zargin sa da karkata akalar naira biliyan 70 mallakar jihar, yayin da gwamnan yace yarfe shugaban EFCC ke masa, saboda yaki bashi cin hancin naira biliyan 2 da ya nema a wurinsa.

Wannan dai ba shine karo na farko da EFCC ke cafke gwamnonin da suka kammala wa’adin mulkinsu ba, domin ko a shekarun baya hukumar ta cafke tsoffin gwamnoni irin su Godswill Akpabio da Ramalan Abubakar da Saminu Turaki da Sule Lamido da Danjuma Goje da Abdullahi Adamu da Jonah Jang da Joshua Dariye da Jolly Nyame da Lucky Igbenedion.

Sai dai a wani bangare, yan Najeriya da dama na bukatar ganin hukumar EFCC ta mayar da hankali sosai akan ministocin gwamnatin Buhari da suka kawo karshen wa’adin mulkin su.

Kungiyoyin fararen hula da dama da kuma masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa na zargin wasu ministocin da saba ka’idar aiki da kuma karkata kudaden gwamnati da dama zuwa mallakar kansu.

Ko a makon jiya, sanda Hukumar ta cafke tsohon ministan wutar lantarkin Buhari, Saleh Mamman wanda ake tuhumarsa da karkata makudan kudaden gwamnati. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here