Gidan da Ganduje zai tare na miliyoyin Naira ya yi gobara a Kano

0
21

Gobara ta kone wani bangaren gidan gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gidan an bayyana cewa, ya lashe makudan miliyoyin nairori wurin ginawa.

Jaridar SOLACEBASE ta bayyana cewa gidan da gwamnan mai barin gado ya koma acikin makonnin da suka gabata a kan hanyar Miagun, bayan Kano Club, Nasarawa GRA, gobara ta lalata wani bangare a yammacin ranar Litinin din da ta gabata.

Majiya mai tushe ta shaida wa SOLACEBASE cewa, gobarar ta tashi ne daga sashin da Dakta Ganduje ke kiwon shanu da sauran dabbobi kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu sakamakon gobarar sannan kuma ta kona wasu kadarori na miliyoyin naira.

“Ba a dai san sanadin tashin gobarar ba, amma ta tashi ne a lokacin da ake yin waldar wasu karafa a gidan, a kokarin da ake na yi wa gidan wasu gyare-gyare don wurin ya zama mazaunin da ya dace da gwamnan mai barin gado,” inji daya daga cikin majiyoyin.

Da yake zantawa da wakilin SOLACEBASE, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya tabbatar da tashin gobarar, ya ce tuni aka shawo kan gobarar a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa gidan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here