Iniesta zai bar Vissel Kobe bayan shekara biyar a kungiyar

0
28

Tsohon dan wasan Barcelona, Andres Iniesta zai bar Vissel Kobe, bayan kaka biyar da kungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Japan.

Mai shekara 39 zai buga wa kungiyar wasan karshe ranar 1 ga watan Yuli a lokacin da ake tsaka da gasar lik ta Japan.

Iniesta, wanda ya shiga karawa uku a canjin ‘yan wasa a kakar nan, bai yi niyar barin Vissel, wadda ta ke ta daya a kan teburi haka da gaggawa ba.

”Na so na kammala kunshin kwantiragin da ta rage min, sannan na fuskanci kalubalen da ke gaba,” in ji Iniesta.

Iniesta ya koma Vissel a 2018, wanda ya yi mata fafatawa 133 da lashe Emperor Cup a 2019 da daukar Japanese Super Cup a 2020.

Ya koma Japan da taka leda, bayan kaka 22 a Barcelona, kungiyar da ya dauki kofi 32 a wasa 674 da ya yi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here