Kungiyar AU na bikin cika shekaru 60 da kafuwa

0
22

Ranar 25 ga watan Mayun 1963 ne dai aka kafa kungiyar tarayyar Africa ta AU  din abinda ke nufin kungiyar na cika shekaru 60 a yau. 

A wannan rana ne dai shugabanin kasashen da ke da ‘yancin kai 32 suka yi wani gagarumin taro da hadin gwiwar kungiyar kwato ‘yancin kasashen Afirka a birnin Addis Ababa da nufin ci gaba da yunkurin kwato yancin sauran kasashen da suka rage karkashin mulkin mallaka da wariyar launin fata.

A yayin taron ne kuma aka amince da kafa kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta OAU.

Bisa al’ada dai akan yi bitar halin da kasashen Afirka suke ciki, yayin da za’a bibiya domin lalubo hanyoyin magance matsalolin da kuma fadada tunani game da yadda za’a ciyar da Nahiyar gaba.

Taron na bana da aka yiwa take da “Afirka muke so” zai sai bakuncin kusan dukannin shugabannin Afirka ko kuma wakilcin su,yayin da za’a fara shine da misalign karfe 10 na safiyar yau agogon GMT.

Kafin taron gani da idon na yau dai tuni aka fara bukukuwan zagayowar wannan rana a shafukan sada zumunta, wanda aka yiwa take da “Afirka ce makomar mu” 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here