’Hare-haren ’yan bindiga na neman hana mu noma’

0
46

Al’ummar wasu kauyuka a yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun koka da yadda hare – haren ’yan bindiga ke neman haramta musu yin noma a bana.

Mazauna kauyukan musamman wadanda ke zaune a masarautar Dan Sadau, da ke karamar hukumar ta Maru, sun shaida wa BBC cewa, duk da bayanan da ke fita na samun saukin hare – haren ’yan bindiga a yankinsu, har yanzu tsuguno ba ta kare ba domin har yanzu akwai wannan matsala a yankunansu.

Wazirin masarautar Dan Sadau, Mustapha Umar, ya shaida wa BBC cewa, a yanzu ’yan bindigar sun hana mutane zuwa gona.

Ya ce, ’’ Tafiyar kilomita guda mutum bai isa ya yi ba, domin maharan sun samu wani waje sun zauna duk sun tare hanya.’’

Shima shugaban kungiyar ’yan sintiri a karamar hukumar Maru, Abubakar Haruna, ya fada wa BBC, a yanzu barayin dajin na neman su mayar da mutanen Dan Sadau da kewaye bayi.

Ya ce, ’’A yanzu kauyuka da ke Dan Sadau da dama na cikin halin kunci da damuwa, saboda hare – haren da ake kawo mana a kowanne lokaci.’’

Shugaban ’yan sintirin, ya ce a yanzu kwata-kwata babu wanda ya isa yaje gonarsa ballantana ya noma abin da zai ciyar da iyalansa.

’Yan bindigar dai sun jima suna kai hare – hare wadannan yankuna, to amma a yanzu lamarin ya munana saboda ga alama suna neman mamaye yankunan ne da nufin sanya ka’idojin gudanar da rayuwa.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ta ‘yan fashin daji wadanda ke kai hare – hare garuruwa da kauyukan jihar baya ga satar mutane don neman kudin fansa da kuma sace dukiyoyin mazauna yankin.

Duk da ikirarin da jami’an tsaro ke yi na shawo kan matsalar ‘yan fashin daji, har yanzu ba su daina kai hare – hare yankunan jihar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here