Kwankwaso ba zai sauya jam’iyya ba -NNPP

0
66
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa jagoranta na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, bai sauya jam’iyya ba.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwankwanso ya gana da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris na kasar Faransa, a baya-bayan nan kuma ya kaddamar da ayyuka a jihohin Ribas da Kaduna tare da jagorantar taron kaddamar da lacca bisa gayyatar zababben gwamnan Jihar Neja.

Al’amarin dai ya janyo cece-ku-ce kan yiwuwar sauya shekarsw zuwa wata jam’iyya.

Sai dai da yake magana a wani taron manema labarai a ranar Asabar kan bikin rantsar da zababben gwamnan Jihar Kano, sakataren yada labarai na jam’iyyar NNPP na kasa, Manjo Agbo, ya ce jam’iyyar NNPP dunkulalliyar jam’iyya ce.

Ya kara da cewa akidar Kwankwanso ita ce jam’iyyar da suke amfani da ita.

A cewar Agbo, Kwankwaso ba zai sauya jam’iyyar ta siyasa ba amma a matsayinsa na jigo na siyasa a kasar nan, kowane dan siyasa yana son ya gana da shi.

A yayin bikin rantsar da Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin sabon gwamnan Jihar Kano a ranar 29 ga watan Mayu, Agbo ya ce Nijeriya na kan kololuwar sabbin gwamnatoci a matakin kasa da jiha, musamman a Jihar Kano, inda babbar jam’iyyarsu ta NNPP za ta karbi mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here