Za mu kammala aikin hako man fetur a jiharmu – gwamnatin Nasarawa

0
95

Gwamnatin Jihar Nasarawa karkashin Abdullahi Sule da ke Tsakiyar Arewacin Najeriya ta ce ba-gudu-ba-ja-da-baya za ta ci gaba da aikin hako danyen man fetur din da aka gano a garuruwan Obi da Keana da ke cikin jihar, abin da ta ce zai bunkasa tattalin arzikin daukacin arewacin kasar.

Gwamnatin ta ce babu wata alamar yaudara dangane da batun gano tare da hako man a jihar domin kuwa mutane sun shaida yadda man ke bulbulowa daga karkashin kasa a wuraren da aka gano a shi a cewarta.

Gwamnatin ta ce, babu yadda za a zuba miliyoyin daloli a wannan aikin sannan kuma a bayyana shi a matsayin yaudara ko kuma siyasa.

A ranar Litinin mai zuwa ne za a rantsar da sabuwar gwamnatin Sule, kuma watakila ‘yan adawa da sauran masu bibiyar lamurran siyasar jihar za su zura ido domin ganin ko sabuwar gwamnatin za ta cika alkwawuranta ko kuma a’a.

A yayin da yake tsokacinsa game da aikin hakar man fetur din, shugaban Jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa, Dr. Jang D.W Mamman ya ce, da ma babu bangaren da gwamnan ya fi kwarewa kamar bangaren harkar man fetur da iskar gas, inda har ya samu horo na musamman a Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here