Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 3, sun kwato makamai a Kaduna

0
100
Kaduna

Dakarun Operation Forest Sanity, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, 2023, sun kashe ‘Yan ta’adda uku tare da kwato makamai da alburusai a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da daraktan hulda da manema labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami, ya fitar, ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a wani harin kwanton bauna da suka kai a yankin dajin Tsohon Kabai-Kubusu da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ya ce sojojin sun kashe ‘Yan ta’addan uku ne a yayin wata musayar wuta tare da kwato bindigu kirar AK 47 guda biyu, mujallu hudu, alburusai na musamman 7.62mm da 16mm da muggan kwayoyi, laya iri-iri da kuma babur guda daya.

Babban hafsan sojin ya yabawa sojojin na Operation Forest Sanity tare da karfafawa jami’an guiwa da su baiwa sojoji bayanai masu inganci da duk abunda ya dace kan ‘yan ta’adda da duk wasu ayyukan ta’addanci a yankinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here