Home Labarai Gwamnatin Kano ta rusa wasu gine-gine a Nasarawa

Gwamnatin Kano ta rusa wasu gine-gine a Nasarawa

0
115
Rahotanni daga Jihar Kano na cewa hukumar kula da tsara birane ta jihar ta gudanar da wani gagarumin rusau.

Kafofin watsa labarai na jihar sun ruwaito cewa hukumar ta gudanar da rusau din ne a gine-ginen da ke jikin katangar filin sukuwa na jihar da ke unguwar Nasarawa.

Rahotanni sun ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da kansa ya jagoranci gudanar da rusau din da misalin karfe biyu na dare.

Wannan rusau din na zuwa ne kasa da mako guda bayan sabon gwamnan ya hau kan karagar mulki.

Tun a baya sabon gwamnan ya sha alwashin waiwayar gine-ginen da aka yi da kuma wuraren da aka siyar ba bisa ka’ida ba a jihar.

Kafafen watsa labarai na jihar da kuma shafukan da ke da alaka da gwamnatin Kano na Kwankwasiyya sun wallafa hotuna da dama na gine-ginen da aka rusa

Mun tuntubi sakataren watsa labarai na gwamnatin Kano Sanusi Bature Dawakin-Tofa domin samun karin bayani sai dai ba mu same shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp