‘Yan kwana-kwana sun ceto mutane 7 da gini ya rushe ya danne su a Kano

0
67

Jami’in hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun samu nasarar ceto mutum bakwai da wata Katangar dakin din adana kaya ta Sufaye da ke a birinin Kano ta rushe ta danne su.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi a Kano, ya ce, lamarin ya faru ne a makon da ya gabata.

Kakakin hukumar ya kara da cewa, sun samu rahoton faruwar lamarin bayan wani mai suna, Bashir Mansur, ya kira layin karta-kwana na hukumar da misalin karfe 05:43 na yamma.

Saminu Ya ce, suna samun rahoton suka yi gaggawar tura jami’ansu zuwa wajen da misalin karfe 05:47, inda ya bayyana cewa, rushewar ginun ta yi sanadin danne mutum bakwai wadanda jami’insu suka ceto su.

A cewarsa, wadanda abin ya rutsa da su duk an ceto su a raye, mutanen sun hada da Abubakar Abdullahi mai shekaru 30 da Abdulsalam Idris mai shekaru 20 sai Usman Abdullahi mai shekaru 20.

 

Sauran sun hada da Usaini Muhammed dan shekara 30 sai kuma Umar Isah mai shekaru 40.

Kakakin ya bayyana cewa, mutum biyar daga cikinsu da suka samu raunuka an garzaya da su zuwa Asibitin kwararru na Abdullahi Wase da ke Kano don a duba tafiyarsu.

Ya ce biyu daga cikinsu da suka samu munanan raunuka an tura su zuwa Asibitin Albarka don a duba tafiyarsu, inda ya ce ana ci gaba gudanar da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here