‘NNPP ta mai da matasa sun zama barayi a Kano’ – APC

0
91

Babbar jam’iyyar adawa a Kano wato APC ta yi Allah wadai kan abin da ta bayyana da cewa “kai farmaki ne kan dukiyoyin al’umma” da gwamnatin NNPP ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ke yi a jihar.

A cikin wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hon. Shehu Maigari ya aika wa manema labarai, APC ta ce ”a yau Kano ta kasance abin tausayawa sakamakon halin da jam’iyyar NNPP ta jefa jihar ciki”.

Jam’iyyar ta APC ta zargi NNPP da gwamnatin Abba Gida-Gida da jefa ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali, inda ta ce harkokin kasuwancin Kano sun tsaya cik.

APC ta kuma yi zargin cewa matakin da NNPP ta ɗauka na rusa wasu wuraren kasuwanci a jihar ya sanya wasu matasa a Kano sun zama ɓarayi, inda ta ce matasan suna yawo da makamai tare da fasa shagunan mutane domin satar kaya.

Haka kuma jam’iyyar adawar ta yi kira ga iyayen yara musamman matasan da ta ce gwamnatin NNPP na amfani da su wajen ɓarnata kayan al’umma, su ja kunnen ‘ya’yan nasu.

Ita dai jam’iyyar NNPP tare da Abba Gida-Gida sun sha alwashin ƙwace wurare da suka ce mallakar al’ummar Kano amma gwamnatin APC ta sayar a lokacin da take kan karagar mulkin jihar.

Kwanaki ƙalilan bayan rantsar da sabon gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara rusa wasu gine-gine a filayen da ya ce na al’ummar Kano ne, a cikinsu har da filin sukuwa da otal din Daula da sansanin alhazan jihar da Babban Filin Idin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here