Yadda soshiyal midiya ke barazana ga lafiyar kwakwalwa

0
75

Kamar sauran miliyoyin mutane a fadin duniya, Brenda Atieno na samun kwanciyar hankali tare da nishadi a duniyar kalle-kalle.

Kwararriya ce a fannin amfani da kafofin sada zumunta na soshiyal midiya, inda ta yi fice a duniyar TikTok da Clubhouse.

Takan shagaltu da hirarraki a shafukan intanet tsawon sa’o’i da dama, inda take nishadantar da mabiyanta da kuma jin dadin yadda suke biye mata.

Sai dai wannan yanayi da ya samo asali a matsayin wata hanya ta samun nutsuwa sannun a hankali ya fara zama jiki.

Halin da Brenda ta tsinci kanta a ciki ya nuna karara yadda mutane ke fafutukar neman suna a shafukan sada zumunta.

A zamanin da ake ciki na duniyar intanet, duba abubuwan da ake watsawa da yabawa da kuma yadawa sun zama wani bangare na rayuwar al’amuran al’umma na yau da kullum.

Ba shakka kafofin soshiyal midiya sun sauya tunaninmu da hanyoyin da muke amfani wajen sadarwa da hulda da kuma yadda muka fahimci duniya.

Brenda ta ce yadda ta fada cikin duniyar shafukan sada zumunta ya zame mata tamkar wata jaraba ta “shan miyagun kwayoyi”.

“Nakan shafe sama da sa’a hudu a rana ina dubawa tare yabawa da kuma yada abubuwan da nake gani a intanet, sannan ni ma nakan watsa wa duniya shirin da na hada ba tare da na ankara da cewa hakan na cinye min rayuwata ba.”

Kullen da aka saka a lokacin annobar cutar korono ya tilasta wa Brenda neman sabbin hanyoyin mu’amala da jama’a, wanda ya kai ta ga duniyar Clubhouse mai jan hankali.

A nan, takan tattauna a kan batutuwa daban-daban da bambancin al’adu da ake da su, sannan ta samu damar kulla alaka mai karfi da mutane daga kowane fanni na rayuwa.

Yanayi ne da ke sanya nishadi – ganin cewa hanya ce da ta cike gibin da ke tsakanin abubuwan da ake iya gani da kuma na badini.

Illar da ke tattare da yin suna a shafukan sada zumunta

Yayin da Brenda ta yi zurfi a shafukan intanet, ta ci karo da bakin duhun da ke tattare da samun suna ko shahara a kafofin na soshiyal midiya.

Ta hadu da masu ci mata zarafi, tare da kai mata hari da munanan kalamai da sukarta ba kakkautawa, kuma kalamansu kan daga mata hankali, sukan sanya ta tunanin lokutan da take makarantar sakandare inda ake yawan kyararta da mayar da ita abar dariya.

“Sukan yi magana game da komai, kama daga gashin kaina zuwa yatsun kafafuna,” in ji Brenda, muryarta cike da jin zafi da azama.

“Muryata wacce ta yi daban da kuma cikakkun labbana sun zama abin da ake yi wa izgili. Ji nake kamar mafarkin da bai karewa.”

Brenda ta gano cewa neman suna babbar masifa ce mai kama da maganin sa maye. Farin cikin samun daruruwa da dubban mabiya masu yaba mata kan duk wani abu da ta yi ya zame mata jarabar da take fama da ita take kuma neman yadda za ta samu hutu daga hakan.

Farin cikin soyayyar da take samu abu ne da ba za ta ki ba, amma a hankali soyayyar da ake mata ke rikidewa zuwa kiyayya da suka.

Komawa duniyar gaske

A wannan lokacin ne Brenda ta yanke shawarar nesanta kanta daga shafukan sada zumunta na tsawon shekara biyu.

 

Wata kwararriya kan kafofin soshiyal midiya ke duba shafukanta Hoto: Reuters

 

Cikin tsananin bacin rai da damuwa, ta dau hanyar sama wa kanta waraka, inda ta kuduri aniyar fita daga cikin duhun da ta nitsar da kanta ciki ta hanyar samun ilimi da kuma nema taimakon kwararru don yakar jarabawar da fada ciki.

“Na sha kuka a asirce,” in ji Brenda, muryarta cike da rauni. “Amma a karshe, na sami karfin gwiwar bayyana lamarin da na fada ciki. A lokacin ne na fara mayar da martani sosai.”

Cike da karfin hali da kuma ilimin da ta samu, Brenda ta sauya rayuwarta, inda ta koma ba da shawarwari kan lafiyar kwakwalwa da kuma hadura da gubar da ke kunshe a shafukan zada zumunta.

Ko da yake, har yanzu dai Brenda tana yaba wa kafofin sada zumunta, inda ta ce a nan ne ta hadu da yawancin kawayenta kuma ta hada kai da mutane da yawa don gina gidauniyar mata.

Abin da fahimta a tsawon lokutan nan su ne, akwai bukatar mutum ya koma baya don duba tasirin da soshiyal midiya ke da shi ga lafiyar kwakwalwa.

Likitan lafiyar kwakwalwa Betty Oloo ta yi gargadi game da yawan shafe lokaci da ake yi wajen kallon allon waya, tana mai ba da shawarar amfani da sa’a biyu a matsayin mafi wayan awannin da mutum zai yi wajen amfani da shafukan a rana, tare da ba idonsa hutu a tsakani don kallon kyawun yanayi.

 

Wani mutum ke yin bidiyon kai tsaye a soshiyal midiya daga garin Mi Mahiu a Kenya. Hoto: Reuters- 2018

 

Binciken da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Amurka ta gudanar ya nuna alakar da ke tsakanin tsawaita lokacin amfani da kafofin sada zumunta da matsalolin lafiyar kwakwalwa, musamman a tsakanin matasa.

Shafe sama da sa’a uku a rana a duniyar kalle-kalle ta yanar gizo na dada kara barazanar jefa mutane cikin hadarin fuskantar matsalolin da suka shafi lafiyar jiki, a cewar masana.

Ana ciin zarafi ta intanet

Da farko dai, yana da muhimmanci a fahimci yanayin cin zarafi ta kafofin sada zumunta.

Oloo ta bayyana cewa cin zarafi hanya ce ta cutarwa da tsoratarwa ko tursasa wani da ake gani a matsayin mai rauni.

Ta ce, a maimakon a tsaya kan dalilan da ke haddasa cin zarafi, yana da muhimmanci a gano masu laifin tare da daukar matakan da suka dace don kare kai. “Sabon da ya zame musu jiki, shi ke cutar da su,” in ji Oloo.

“Da zarar sun fahimci abin da kake tsoro, sai su dada matsowa kusa. Rufe su daga shafinka ko fallasa su da kuma mika rahoto ga hukumomi na taka rawa wajen sanya su shiga taitayinsu.”

Oloo ta jaddada cewa masu cin zarafi ta yanar gizo galibi suna fama da matsalar rashin zaman lafiya kuma suna bukatar taimakon kwararru su ma.

Masana sun ce don magance mummunan tasirin gubar da ke tafe da yawan sabo da soshiyal midiya, ayyukan motsa jiki na taka muhimmiyar rawa da kuma farfado da abubuwan da aka fi sha’awar yi na yau da kullum.

Hakan na taimaka wa wajen sake wasu sassan gabobin jiki na hormones kamar endorphins da serotonin da dopamine.

Yayin da muke kara samun kuzari, kwakwalwarmu za ta kara samun nutsuwa sannan muna yakar kadaici, a cewar masana ilimin halayyar dan adam.

Bugu da kari, hulda ta kai tsaye da mutane da yin tafiye-tafiye da kuma bincike kan abubuwan da muke kewaye da su, za su taimaka wajen kara inganta hanyoyin tunaninmu.

Babu shakka intanet yana ba da dimbin ilimi da hadin kai, amma yawan amfani da shi na iya zama illa, in ji masana.

Sannan yana da mahimmanci a gano shafuka a intanet da kuma daidaikun mutane daga kafofin sada zumunta da ke da mummunan tasiri a kan lafiyar kwakwalwarmu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here