‘Yar shekara 3 ta zama miloniya daga zuwa sayen burodi

0
115

Masu iya magana sun ce ‘Dare daya Allah kan yi Bature” wanda haka ke nuna ikon Ubangiji na sauya halin da dan Adam ke ciki musamman na matsi ko tsanani da rashi zuwa na dukiya da wadata a cikin kankanin lokaci; kamar yadda hakan ta faru ga wata ’yar karamar yarinya da ta je sayen burodi kuma hotonta da aka dauka ya sauya rayuwarta da na iyayenta.

Lamarin ya faru ne a kasar Afirka ta Kudu ga yarinyar mai shekara uku mai suna Lethukhanya Mjaja da iyayenta suka aike ta sayo burodi, bayan ta sayo a hanyarta ta dawowa gida sai ta tsaya ta shiga cikin wani ruwa da ke kwanciya a kan hanya tana wasa.

Sai wani kawunta mai sana’ar daukar hoto ya gan ta, kuma cikin wasa ya dauki hotonta rike da burodi tana dariyar wasan da yake yi mata, ya kuma sa a shafinsa na Intanet.

Kafin a ce kwabo, sai hoton ya yi farin jini inda aka riqa yada shi a shafukan sada zumunta na kasar.

Abin ya faranta wa kamfanin burodin rai, inda a cewar wani rahoto, bayan da suka yi amfani da hotonta a manyan allunan talla da kuma motocinsu na sayar da burodi hakan ya kara musu farin jini da kasuwa, don haka sai suka yanke shawarar yin kyauta ta musamman ga yarinyar da iyayenta.

Sun nemi iyayen yarinyar da mai hoton da kuma yarinya suka musu kyauta mai tsoka na makudan kudin yin hoton
yarinyar nan a manyan allunan talla na kasar. Kuma haka aka yi.

Shikenan sai labari ya sha bamban ga wannan yarinya da kawunta mai hoto da kuma iyayenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here