Babu dokar da ta ce sai ina da shaidar gama NYSC za a nada ni minista – Hannatu Musawa

0
282

Ministar Al’adu ta Najeriya Hannatu Musawa ta musanta zargin da ake yi mata na karya dokar ƙasa bayan naɗa ta a muƙamin duk da cewa ba ta kammala hidimar ƙasa ta NYSC ba.

Cikin wani martani da ta fitar a yau Lahadi, ministar ‘yar jihar Katsina a arewacin Najeriya ta ce “babu wata doka da na karya”.

“Dole ne na faɗa cewa babu wata doka a Najeriya da ta ce shugaban ƙasa ko wata hukuma ba za su iya naɗa mutumin da yake hidimar ƙasa a muƙami na siyasa ba,” in ji ta.

Sai dai, mai magana da yawun hukumar National Youth Service Commission (NYSC), Eddy Megwa, ya faɗa wa Daily Trust cewa “ta karya doka kuma muna duba yiwuwar ɗaukar matakin da ya dace” a kanta.

A ranar Litinin 21 ga watan Agusta Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Hannatu – wadda yanzu haka take gudanar da hidimar ƙasar a Abuja – a matsayin minista tare da sauran mutum 45.

Hannatu ta tabbatar da cewa tun a 2001 aka tura ta hidimar ƙasar zuwa jihar Akwa Ibom amma ta ɗage aiwatarwa sai a 2023 ta ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here