Likitocin jihar Zamfara na barazanar rufe asibitocin gwamnati kan rashin albashi

0
249

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako guda ta biya ma’aikatan lafiya 17 albashinsu na wata hudu da sauran ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Yarima Bakura ko kuma su shiga yajin aiki.

Shugaban NMA na jihar, Dakta Sanusi Bello, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, ya kuma bayar da misali da albashin dukkan likitocin asibitin na watan Yuli 2023, da alawus na wata takwas ga kwararrun likitoci da ba a biya, wanda ya sa suka daina aiki.

Bello ya ce kungiyar ta yanke shawarar bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin jihar Zamfara domin ta magance wadannan bukatun.

Ya kara da cewa ƙungiyar a Zamfara za ta ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 4 ga Satumba, 2023, idan har gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.

Shugaban ya yi gargadin cewa matakin zai kai ga rufe dukkanin asibitocin da suka hada da asibitocin gwamnatin tarayya da asibitocin jiha da asibitoci masu zaman kansu da kuma janye duk wani aikin lafiya da na hakori da duk likitocin jihar Zamfara ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here