APC ta jefa ‘yan Najeriya cikin ukuba – PDP

0
151

Babbar jamiyyar adawa PDP ta zargi jamiyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da jefa al`ummar ƙasar cikin ukuba.

Jamiyyar ta zargi shugaba Tinubu da gazawa wajen inganta rayuwaryan Najeriya ciki har da janye tallafin man fetur da karya darajar naira da kuma gazawa wajen shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta ta fuskar tabarbarewar tsaro, lamarin da ya jefa al`ummar ƙasar cikin kunci.

A tattaunawarsa da BBC, mataimakin kakakin jam`iyyar PDP na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya ce lamarin ya jefa ƴan ƙasar fiye da mutum miliyan dari da hamsin cikin hali na yunwa a watanni biyun da suka wuce, wadda ta bayyana a matsayin sakamakon munanan manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.

Sai dai APC ta musanta wannan zargin tana mai cewa adawa ce kawai daga jam’iyyar PDP.

Daraktan yada labarai na jam`iyyar APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa PDP ɗin ce ta jefe Najeriya a mawuyacin halin da ake ciki tun asali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here