Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Kwankwaso

0
324

Kwamitin amintattu na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta sanya wa Sanata Rabi’u Kwankwaso, shugaban jam’iyyar na kasa dakatarwa na tsawon watanni shidda, saboda cin zarafin jam’iyyar da ya yi a rahoton jaridar TVC.

Bayan zabukan 2023, rikici ya ci gaba da yawo a cikin jam’iyyar cikin lumana, tare da zarge-zarge a tsakanin bangarori daban-daban.

Ya zuwa yanzu dai hakan ya kai ga dakatar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa kuma shugaban jam’iyyar na kasa baki daya.

Wannan ci gaban ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sakataren Yada Labarai na kasa da wasu mambobi a baya, hukuncin da kwamitin amintattu na jam’iyyar suka zartar.

Tun da farko dan takarar gwamnan jihar Benuwe na jam’iyyar ya fice daga jam’iyyar saboda rikicin cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here